Hukumar kula da masu shige da fice ta fara wayar da kan al’umma na shekarar nan a kokarin da take na inganta ayyukanta.

Mai magana da yawun hukumar Sunday James, ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar a Abuja.

Ya ce hukumar ta fara shirin ne domin wayar da kan ma’aikatanta da sauran al’umma a cikin kwanaki 3 na wannan makon. 

James ya ce tsarin da hukumar ta fito dashi na daga cikin shirin ta na janyo al’ummomin kasa a jiki ta yadda za su saukaka mata ayyukan da ta sanya a gaba.

A cewarsa hukumar tafi so ta maida hankali kan wayar da kawunan al’umma ta yadda za su bada gudunmawar da ake bukata, wanda shi ne makasudin kirkiro da shirin na wayar da kai.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *