Ministan ayyuka da samar da gidaje Babatunde Fashola, ya karbi cekin kudin lamuni daga Sukuk na sama da naira billiyan dari da 62, domin ci gaba da gyaran hanyoyi a fadin kasar nan.

A lokacin da take bada cekin kudaden Ministar kasafi da tsare-tsare Zainab Ahmad ce ta samar da ababen more rayuwa shine ginshikin farfado da tattalin arziki.

Ta ce za a ci gaba da samar da ayyukan more rayuwa ne domin magance dukkan matsalolin dake kawo cikas a kokarin da ake na bunkasa tattalin arzikin kasa.

Ta ce da wannan ci gaban da aka samu na lamuni daga Sukuk da kuma sauran kudaden da gwamnatin tarayya ta tura, za su taimaka wajen farfado da tattalin arzikin cikin gaggawa.

A nasa jawabin Fashola ya ce wadanda suka zuba jari a asusun na Sukuk sune ginshikai, a cewarsa wannan na daga cikin yarda dake tsakanin asusun da gwamnatin tarayya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *