Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya jaddada kudurin da gwamnatinsa ke da shi na janyo ra’ayin masu zuba jari a jihar domin bunkasa tattalin arziki.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a Lafiya babban birnin jihar lokacin da ‘yan uwa da abokan arzikin Sakataren gwamnatin jihar suka kai masa ziyarar godiya na nadin da ya yiwa Aliyu Ubandoma.

Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da yin iya bakin kokarin ta tare da samar da yanayi mai kyau da zai janyo hankalin masu zuba jari na gida da kasashen ketare.

Sannan ya yabawa tawagar da ta kai masa ziyarar, tare da basu tabbacin gwamnatinsa za ta ci gaba da tafiya da dukkanin bangarori, ba tare da la’akari da banbancin siyasa ko addini ba.

Ya kuma yabawa tsohon gwamnan jihar Tanko Almakura, bisa irin namijin kokari da ya yi na aikin raya kasa, tare da tabbatar da cewa zai ci gaba da mutunta shi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *