Hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta ce mutane 562 sun sake kamuwa da cutar korona cikin sa’o’i 24 a Najeriya, wanda ya kawo yawan mutanen da suka kamu da cutar 37,225.

Hukumar ta bayyana hakan ne a shafin ta na twitter a daren Litinin.

Ta ce cutar  ta sake kashe mutane 12 a faɗin Najeriya.

Ƙididdigar da hukumar ke fitarwa a kullum ya nuna cikin mako ɗaya cutar ta kashe mutum kusan 60 daga 13 ga watan Yuli zuwa 20 ga wata.

Alƙalumman sun kuma nuna yanzu cutar ta yi ajalin mutane 801, ƙasa da watanni biyar bayan ɓullarta.

NCDC ta kuma nuna cewa masu korona 228 ne suka warke daga korona har kuma an sallame su ranar Litiin don komawa gida cikin iyalansu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *