Mukaddashin shugaban Hukumar NDDC masu kula da yankin Naija Delta ya kamu da farfadiya a gaban kwamitin bincike na majalisar wakilai.

Wanda suke tuhumarsa da salwantar da fiye da naira biliyan 40 a hukumar sa.

Jim kadan bayan gurfanar sa a gaban kwamitin don amsa tambayoyi, sai ya kwantar da kansa ya fara farfadiya.

Wannan farfadiya dai ta tilasta katse zaman majalisar sakamakon hargitsi da ya biyo baya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *