Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya daura alhakin hauhawar miyagun ayyukan ‘yan bindiga da ‘yan ta’addan Boko Haram da ke addabar arewa akan ‘yan siyasa masu son takara a shekara ta 2023.

Wannan dai ya na zuwa ne, bayan ‘yan bindiga a jihar Zamfara sun mika bindigogi 50 a makon da ya gabata, don amincewa da karbar shanu biyu da gwamna Matawalle ya ce zai bada ga duk wanda ya kai bindiga daya.

Ya ce wadannan ‘yan siyasar sun yarda cewa ta hanyar daukar nauyin ‘yan bindiga da sauran ‘yan ta’adda ne kawai za su iya bata wa mulkin shugaba Buhari suna don samun damar mulki.

Masari ya bayyana haka ne, yayin wani taro da ya yi da shugabannin jam’iyyar APC na guduma da kananan hukumomi na jihar Katsina, inda ya ce da yawa daga cikin ‘yan bindigar da ‘yan Boko Haram da ke kai hari a Nijeriya su na bin umarnin wasu ‘yan siyasa ne.

 Ya ce da yawa daga cikin hare-haren ‘yan bindiga da Boko Haram da yankin arewaci ke fuskanta, duk wasu ‘yan siyasa kuma makiyan gwamnatin APC ke daukar nauyi a matakin tarayya da jiha.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *