Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya gana shugaban rundunar sojin kasa ta Nijeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai.

A baya dai shugaban kasa Buhari ya gana da shugabannin hukumomin tsaro, inda ya ja kunnen su tare da tsawata masu a kan sauke nauyin da ya rataya a wuyan su.

Shugaba Buhari, ya ce dole sai shugabannin tsaron sun kara kokari wajen kawo karshen matsalar rashin tsaro da ta addabi Nijeriya.

Buhari ya kuma nuna rashin gamsuwa da rashin hadin kai a tsakanin shugabannin hukumomin tsaron.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *