Wata gobara ta tashi a sabon ginin da aka kammala na ofishin hukumar tattara haraji ta kasa reshen jihar Katsina.

Gobarar ta tashi ne a ofishin hukumar da ke kallon filin wasa na Muhammadu Dikko da misalain karfe 12 da minti 08 na ranar Litinin din nan, sai dai jami’an hukumar kashe gobara na jihar sun yi kokarin kashe ta.

Kimanin makonni biyu kenan da wata gobara ta tashi a babban bankin Nijeriya da ke jihar Gombe, lamarin da ake ganin ya shiga jerin gobara da aka samu a ma’aikatun gwamnati a fadin Nijeriya cikin ‘yan watannin nan.

A ranar 8 ga Afrilu na shekara ta 2020, Ginin da aka fi sani da Gidan baitul-mali da ke kusa da helkwatar hukumar ‘yan sanda da ke unguwar Garki a Abuja ya yi gobara.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *