‘Yan bindiga sun kashe sojojin Najeriya uku yayin wata arangama a wani daji da ke ƙaramar hukumar Jibiya a jihar Katsina.

Wata sanarwa da helkwatar tsaron Nijeriya ta fitar, ta ce lamarin ya faru ne yayin da Rundunar Sahel Sanity tare da haɗin gwiwar sojojin sama su ka kutsa cikin dajin Jibiya domin kai wa ‘yan bindigar hari.

Sanarwar ta ce sojojin sun kashe ‘yan bindiga 17, yayin da wasu da dama su ka tsere da harbin bindiga a jikin su.

Jihar Katsina na ɗaya daga cikin jihohin da ‘yan bindiga ke ci-gaba da cin Karen su babu babbaka, inda al’ummar wasu ƙauyuka da su ka hada da Batsari da Dutsinma da Jibiya da Faskari ke cewa kaso mai yawa na manoman yankin ba su yi ko sharar gonakin su ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *