Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bukaci taimakon Hukumar raya kasashe ta majalisar dinkin duniya UNDP, domin samo wanda zai nada a matsayin mai ba shi shawara na musamman a kan ayyukan raya kasa.

Sabon jami’in da za a nada dai, zai yi aiki ne a karkashin shugaban ma’aikata na Fadar Shugaban kasa wajen taimaka wa gwamnati aiwatar da manufofin ta.

Hukumar UNDP, ta ce fadar shugaban kasa na kokarin sake fasalin aikin ofishin shugaban Ma’aikanta daga wanda ake yi wa zargin hannu a harkokin siyasa da rashin inganci wajen sauke nauyin da ke kan sa, sabanin yadda ya ke a baya, zuwa wanda zai yi aiki tukuru wajen cimma manufofin gwamnati.

Ta ce za a kammala karbar takardun masu neman aikin daga ranar 19 ga watan Yuli, kuma wanda y  a yi nasara zai kwashe tsawon watanni 12 daga ranar 3 ga watan Agusta na wannan shekarar zuwa watan Agustan shekara ta 2021.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *