Binciken da rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta yi a Katsina ya gano cewa, yaran da su ka mutu bayan fashewar wani abu a gona sun tsinci Gurnetin soji ne, wanda su ka rika wasa da shi ba tare da sun san ko menene ba.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda na jihar Katsina Gambo Isa ya sanar da sakamakon binciken game da lamarin da ya auku a kauyen ‘Yammama da ke karamar hukumar Malumfashi.

A baya dai mazauna yankin sun ce mutane 6 su ka mutu, sai dai rundunar ‘yan sanda ta ce mutane 5 ne su ka rasa rayukan su.

Bayanai sun ce yaran 11 da lamarin ya rutsa da su sun je gona ne domin yin ciyawar dabbobi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *