Daya daga cikin mutane uku da aka kama da laifin yawan kisan jama’a a yankin Akinyele da ke Ibadan, ya ce ana ba shi Naira 500 da abinci ne a duk lokacin da ya kashe mutum.

Mai laifin, wanda matashi ne dan shekaru 19, ya na daga cikin masu laifi 19 da kwamishinan ‘yan sanda na jihar Oyo Nwachukwu Enwonwu ya gabatar a helkwatar ‘yan sanda, yayin da sauran su ka hada da ‘yan fashi da makami da barayin babur da masu aikata fyade da sauran su.

Matashin, ya ce wani boka ne ya ke tura shi ya kashe mutane, inda a duk lokacin da zai fita domin aikata kisa Bokan ya kan ba shi wasu tarkace tare da koya ma shi karatun wasu kalamai da zai rika karantawa don kada a kama shi.

Ya ce ya na amfani da Cebur ne wajen buge mutumin da zai kashe, kuma da zarar mutum ya fadi ya ga jini ya na fita daga jikin sa sai ya fara karanta kalaman da Bokan ya koya ma shi.


Kwamishinan ‘yan sanda, ya ce sun samu nasarar kama matashin ne ta hanyar bin diddigin wayar daya daga cikin mutanen da ya kashe mai suna Azeezat Shomuyiwa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *