Mai tsawatarwa na majalisar wakilai, Mohammad Tahir Monguno, ya ce dakarun sojin Nijeriya sun gaja wajen kawo ƙarshen ‘yan ta’addan Boko Haram.

Monguno ya bayyana wa manema labarai haka ne, yayin da ya ke jawabi a kan binciken da majalisar wakilai ke yi bayan sanar da murabus na wasu sojoji 365 farat ɗaya.

Ya ce rashin samun karin girma akai-akai musamman ga kananan jami’an soji ya sa basu samu kwarin gwiwa da kishin kasa.

Ya kara da cewa matsalar ta janyo dakushewar aikin da rashin kuzarin sojoji, waɗanda kuma ke shafar yaƙin da Nijeriya ke yi da Boko Haram.
Ya ce wasu dalilan rashin yin nasara a yaƙin akwai sanyin jiki da rashin kuzari na manyan sojoji, wanda su na ganin ya kamata su ƙure muƙaman aikin soja amma ba su ƙure ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *