Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da ranar komawa aiki ga ma’aikata a fadin jihar.

A cikin wata sanarwa da gwamnatin ta wallafa a shafin ta na Twitter, ta ce ma’aikatan gwamnati da ke mataki na 14 za su koma bakin aiki daga ranar Litinin 20 ga watan Yuli na shekara ta 2020.

Sanarwar, ta ce wajibi ne ga dukkan ma’aikatan su zama masu bin dokar da mahukunta a bangaren kiwon lafiya su ka shimfida, sannan masu mataki na 14 zuwa sama za su rika zuwa aiki ne a ranakun Litinin da Laraba da kuma Juma’a.

Daga masu mataki na bakwai zuwa na 13 kuma za su koma aiki daga ranar Talata, kuma za su rika zuwa aiki ne a ranakun Talata da Alhamis daga karfe 9 na safe zuwa uku na yamma.


Kaduna dai ta na cikin jihohin da annobar korona ta fara bulla a yankin arewa, kuma ta na cikin jihohin da su ka fi daukar tsauraran matakan kariya a fadin Nijeriya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *