Ma’aikatar kula da harkokin ilimi ta ba makarantu masu zaman kansu zuwa ranar 29 ga watan Yuli su cika ka’idojin da ta gindaya kafin sake bude makarantu.

A cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun darakatan yada labarai na ma’aiktar Ben Bem Goong, ta ambato karamin ministan ilimi ya na cewa, matakin ya na zuwa ne bayan ganawa da masu ruwa da tsaki da su ka hada da ma’aikatar lafiya da cibiyar hana yaduwar cututtuka ta kasa da sauran su.

Sanarwar, ta ce ma’aikatar ilimi ta gana da hukumar shirya jarabawar kammala karatun sakandare WAEC, kuma ta amince ta tuntubi wasu kasashe 4 game da sauyin lokacin jarabawa.

Ma’aikatar ilimin, ta ce kafin a bude makarantu dole sai ma’aikatun ilimi na jihohi sun gana da ma’aikatar ilimi ta kasa, tare da tattaunawa da kwamitin yaki da cutar coronavirus ta kasa da saura masu ruwa da tsaki, da zummar yin nazari a kan abubuwan da ake bukata.
Kowace jiha dai dole a samar da wani shirin kula da lafiya a makarantu a karkashin jagorancin wani jami’i a jihar, yayin da kowace makaranta za ta nada jami’in da zai rika hulda da babban jami’in a matakin jiha.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *