Gwamnatin Amurka ta bukaci wasu ‘yan Nijeriya sama da 370 su fice daga kasar sakamakon aikata wasu laifuffuka da su ka hada da karya dokar shige da fice da laifuffukan da ke da nasaba da yanar gizo.

Rahotanni sun ce an tabbatar da laifuffukan ne a kotunan da ke Jihohin Texas da New York da California, da kuma wasu karin Jihohin kasar daga watan Janairu zuwa Yunin wannan shekara.

Wata majiya ta ce alkaluman hukumomin Amurka sun bayyana cewa, ‘yan Nijeriya sama da dubu 3,000 aka kora daga kasar bayan kotuna sun same su da laifi a cikin shekaru 15 da su ka gabata, yayin da a cikin watanni 6 na wannan shekarar aka samu ‘yan Nijeriya 335 da su ka shiga Amurka ta hanyar da ba ta dace ba, ko kuma su ka cigaba da zama a kasar bayan karewar bizar su.


Mutanen 376 da za a kora dai su na daga cikin ‘yan Nijeriya 901 da yanzu haka ake tsare da su a wurare daban-daban da ke kasar Amurka.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *