Rahotanni da muke samu daga jihar Katsina na cewa wani abin fashewa ya yi sanadiyyar mutuwar yara 6 yayin da wasu 5 suka jikkata a kauyen ‘Yammama na karamar hukumar Malumfashi.

Majiyar ta ce abin fashewar ya tashi ne a ya yin da yaran suka je neman abincin dabbobi a bayan gari.

Rundunar ‘yansandan jihar Katsina ta hannun Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan Sandan jihar Isah Gambo ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ‘yan sanda na ci gaba da bincike a kan lamari.

A baya dai, yankuna na Faskari da Sabuwa da karin wasu sassan jihar Katsina na fama da ayyukan ‘yan bindiga da ke kai hari a kauyuka musamman wadanda ke makwabtaka da daji.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *