Wasu rahotanni na cewa sama da ‘yan Nijeriya dubu 70 ne su ka tsere zuwa Jamhuriyar Nijar, sakamakon hare-haren ‘yan bindiga da ya addabi al’ummar arewa maso yamma.

Rahotannin sun ce baya ga rasa rayuka da dukiya da muhallan su, ‘yan gudun hijra a jihohin Zamfara da Katsina da Sokoto sun yi alhinin yadda gwamnatin Nijeriya ta yi watsi da su.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya, ta ce akalla ‘yan Nijeriya dubu 23 ne su ka tsere zuwa kasar Nijar domin kare rayukan su saboda ‘yan bindiga sun tagayyara su.

Daya daga cikin matasan da su ka gudu Nasuru Lawal ya bayyana wa manema labarai cewa, Sojojin Nijerya sun yi watsi da su yayin da na Nijar ke kai masu dauki.

Ya ce tun lokacin da rikicin ya fara ba su ga jami’in Nijeriya ko daya ba, Sojojin Nijar ne ke kai masu dauki domin su na da kyakkayawar alaka da su.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *