Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan, da na majalisar wakilai Femi Gbajabiamila sun ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari domin tattaunawa kan takaddama da aka samu a tsakanin ‘yan majalisar da karamin ministan kwadago.

Mai ba shugaban kasa a kan shafukan sada zumunta Bashir Ahmad, ya bayyana haka.

Idan dai ba a manta ba, a ranar Talatar da ta gabata, majalisar dattawa ta shiga ganawar sirri ta gaugawa a kan hukuncin ma’aikatar kwadago na ci-gaba da shirin daukar ma’aikata dubu 774.

‘Yan majalisar dokoki na tarayya dai sun zargi Keyamo da kwace shirin daukar ma’aikatan daga hukumar daukar ma’aikata ta kasa, wadda ta samu naira biliyan 52 domin aiwatar da shirin.

Sai dai Keyamo ya shaida wa manema labarai cewa, Shugaba Buhari ya bukaci ya ci gaba da shirin daukar ma’aikatan ba tare da la’akari da matsayar majalisun dokokin ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *