Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya tura shugabannin tsaro zuwa yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya, domin ganawa da masu ruwa da tsaki  a kan matsalar tsaro da ake fuskanta.

Shugaban ‘Yan Sandan Nijeriya Muhammad Adamu ya tabbatar da haka, ya ce ganawar da masu ruwa da tsakin zai sake nazari a kan tsare-tsaren tsaro da bijiro da sabbin dabarun kawo karshen hare-hare da tadada zaune tsayen da ya mamaye Arewa maso Yamma.

Muhammad Adamu ya bayyana haka ne, yayin da shugabannin tsaron su ka kai ziyarar ban-girma a Fadar Mai Martaba Sarkin Gusau Ibrahim Bello.

Ya ce kokarin da gwamnatin tarayya ke yi don magance matsalar tsaro ba a jihar Zamfara kawai ya tsaya ba, har ma da sauran jihohin Arewa maso Yammacin Nijeriya baki daya.

Shugaban ‘yan sandan ya cigaba da cewa, sun je Zamfara ne saboda Shugaba Buhari ya ba su umarni, tare da gargadin cewa su tabbatar sun kawo karshen matsalar rashin tsaro a yankin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *