Shugaban Majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, ya ce duk da dimbin biliyoyin nairori da gwamnatin tarayya ke narkawa a asusun Hukumar Bunkasa Yankin Neja-Delta, har yau hukumar ba ta aiwatar da wani aikin kirki da za a jinjina mata ba.

Gbajabiamila ya bayyana haka ne, a wajen zaman Kwamitin Majalisar Mai Binciken Badakalar Kudaden da aka kashe a wata mummunar harkallar biliyoyin kudaden da ake ci-gaba da fallasawa.

A cikin shekara ta 2019 ne, Shugaba Buhari ya bada umarnin a yi binciken filla-filla na yadda aka narkar da kudaden hukumar NDDC tun daga shekara ta 2001 har zuwa ta 2019.

Hukumar raya yankin Neja Delta dai ita ce gwamntin tarayya ta dora wa alhakin bunkasa jihohin yankin, wadanda su ka hada da Bayelsa da Rivers da Cross River da Edo da kuma Ebonyi.

Daga cikin alhakin da aka dora ma hukumar, akwai ilimantar da matasan yankin, da ba su horo da sama masu ayyukan dogaro da kai don su watsar da tashe-tashen hankulan da su ka hada da fasa bututun mai da kai wa masana’antun hako danyen mai hare-hare.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *