Jam’iyyar APC ta zabi gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello a matsayin jagoran kwamitin zaben fidda gwani na tikitin takarar kujerar gwamnan jihar Ondo, wanda za a gudanar ranar Litinin, 20 ga watan Yuli.

Kwamitin riko na jam’iyyar APC na kasa, ya kuma zabi Emperor Chris Baywood Ibe ya jagoranci kwamitin mutane 9 da za su daukaka kara a kan zaben.

Bayanin Hakan ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakin mai magana da yawun jam’iyyar Yekini Nabena ya fitar a Abuja.

Nabena, ya ce nade-naden sun biyo bayan amincewar da shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC na kasa Mai Mala Buni ya yi.

‘Yan kwamitin kuwa sun hada da Olorogun o’tega Emerhor, da Alwan Hassan, da Chief Samuel Sambo, da Hajiya Binta Salihu, da Mr. Emma Andy, da Dr. Adebayo Adelabu, da Abdullahi Aliyu da kuma Mrs. Margret Ngozi Igwe.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *