Daliban makarantun gaba da Sakandire da suka hada dana jami’o’i da kwalejojin kimiyya dana Ilimi sun ba gwamnatin Najeriya makwanni 2 ta bude makarantu ko su fita zanga-zanga.

A taron da suka yi ta kafar sadarwar Zamani, Daliban sun bayyana rashin jin dadin hana kannensu dake ajin karshe na sakandire rubuta jarabawar WAEC inda suka ce za’a iya Rubuta jarabawar ba tare da karya dokar matakin kariya daga cutar ba.

Gwamnatin tarayya ta rufe makarantun ne tun a watan Maris sakamakon bullar cutar korona, da ta addabi duniya.

Sun kuma bayyana cewa lura da yanda lamura ke tafiya, cutar korona ba wacce za’a iya maganinta nan nan gaba kadan bane, dan haka kawai a koma Makaranta.

Daliban sun kuma yi kira ga gwamnati da ta dakatar da Albashin malaman jami’ar saboda ci gaba da goyon bayan rufe makarantu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *