Runduna ta musamman dake yaki da ayyukan ta’addanci da ake yiwa lakabi da Operation Sahel Sanity ta ce ta kashe ‘yan ta’adda 6 a wani hari da suka kai a maboyarsu dake tsaunin Komini a garin Rukuduwa dake karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.

Mai rikon mukamin jami’in kula da harkokin yada labarai da hulda da jama’a na rundunar Benard Onyeuko, ya ce jami’an sojin sun yi nasara akan ‘yan ta’addan ne a musayar wuta da aka yi, inda bayan sun kashe wasu, wasu kuma suka tsere da raunukan bindiga.

A cewarsa rundunar ta kuma kai dauki a wani barazanar da ‘yan ta’adda suka yin a sace shanu a Kasele dake karamar hukumar Batsari dake jihar Katsina.

Ya ce an kama wani mai ba ‘yan ta’addan bayanan sirri mai zuwa Muhammad Lawali Maikudi Modu a garin Marabar Dan Ali a karamar hukumar Gusau.

Onyeuko ya ce rundunar ta kwato bindiga kirar AK47 guda 1, da kwanson alburusai guda daya da kuma mashinan hawa 34 da sauran su.

Sannan a baya ta kama wani Addu Abubakar a karamar hukumar Talata Mafara dake jihar ta Zamfara.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *