Majalisar Dattawa ta bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Ma’aikatar Kwadago da ta kafa wani kwamiti da zai yi dubi akan batun kiyata shekaru domin daukan ma’aikata a Najeriya.

Kiran ya fito ne daga bakin dan majalisa Ibrahim Gobir a lokacin zaman Majalisar a Abuja.

Gobir ya ce batun kiyata shekaru na 35 da ake sanyawa a yayin da za a dauki ma’aikata a hukumomi da ma’aikatu na jawo tsaiko ga al’ummomin Najeriya musammamn yadda yawan rashin aikin ya yi yawa a kasa.

Ya ce matashi zai shafe kusan shekaru 10 yana Jami’a sannan ya fito ya yi ta fafutukar neman aikin, kuma shekarun sa ba raguwa suke yi ba wanda hakan yasa dayawan matasa ke karyan rage shekaru domin samun damar da za a dauke su aiki.

Daga karshe ya bukaci wadanda alhakin hakan ya rataya a wuyansu da su dubi wannan batu da muhimmanci tare da daukan matakan da suka dace cikin gaugawa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *