Likitoci a Jihar Legas sun janye yajin aiki na gargaɗi da suka fara kwanaki uku da suka gabata a yau Alhamis.

Likitocin sun shiga yajin aikin ne saboda albashin da ba a biya su ba da kuma kayan kariya a duk lokacin da suke aikin kula da marasa lafiya musamman masu dauke da cutar korona.

Shugaban ƙungiyar likitocin, Oluwajimi Sodipo ya ce yajin aikin nasu ya yi amfani domin kuwa sun yi nasara wurin jawo hankalin mahukunta game da abubuwan da ke damunsu sannan kuma gwamnati na shirin tattaunawa da su.

Yajin aikin likitocin na zuwa ne a daidai lokacin da ake kara samun karuwar masu dauke da cutar korona a Najeriya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *