Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar Kaduna ta ce ma’aikatan kula da lafiya dari da 44 ne aka tabbatar da sun kamu da cutar korona a fadin jihar.

Shugaban hukumar Iliyasu Neyu, ne ya bayyana haka a wajen taron da hukumar ta gudanar da kwamiti na musamman dake dakile yaduwar cutar a fadin jihar.

Ya ce daga cikin ma’aikatan lafiyar da suka kamu da cutar a jihar daya ya rasa ransa, yayin da wasu suka warke.

Neyu ya ce zuwa wannan makon, mutane dubu 6 da dari 7 da 47 ne aka yi tunanin sun kamu da cutar, tun bayan bullarta a jihar a ranar 27 ga watan Afrilun wannan shekarar.

A cewarsa a cikin mutanen da aka yiwa gwaje-gwaje tun a lokacin, an tabbatar da mutane dubu 1 da 16 sun kamu da cutar, kuma nan take aka killace su.

Neyu ya ce zuwa yanzu akwai mutane 348 da suke dauke da cutar da ake kula da su a cibiyoyin da ake killace masu dauke da cutar yanzu haka a Kaduna.

Ya ce a yanzu haka cutar ta bazu zuwa kananan hukumomi 15  dake fadin jihar, inda karamar hukumar Kaduna ta Arewa ke kan gaba na yawan masu dauke da cutar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *