Majalisar zartaswa ta Najeriya ta fitar da daftarin sama da naira triliyan 12 da za a kashe daga shekarar 2021 zuwa 2023.

Karamin ministan kasafi da tsare-tsare Clement Agba, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron majalisar zartaswar da shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Agba ya ce za a yi amfani da kudaden ne wajen manyan ayyuka da kanana, ciki har da aikin hakowa tare da sarrafa man fetur wanda zai ci naira miliyan 1 da dubu dari 6 ko wacce ganga.

Ya ce akwai ragi sosai a kudin da za a kashewa bangaren hakowa da sarrafa man idan aka kwatanta da na farkon wannan shekarar da aka fitar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *