Ministan Sadarwa Aliyu Isa Pantami ya ce nan gaba kadan kudin da jama’a ke kashewa wajen yin kira a wayar salula zai ragu da kashi 40 cikin dari bayan matakan da gwamnatin tarayya ta dauka.

Ministan ya bayyana cewa za a ga ragi a kudin waya bayan sun kwadaito da masu zuba hannun jari zuwa Najeriya.

Ya ce gwamnatin ta shawo kan kalubalen da ake samu na kudin jawo igiyoyin RoW, da kuma tsare kayan aiki.

Pantami ya yi wannan jawabi ne a wajen bude bikin koyon aiki da hukumar NITDA ta shirya wanda za ayi tsawon mako guda ana yi a birnin tarayya Abuja.

Ministan ya kara da cewa ci gaban da su ka kawo wajen kayan aikin sadarwa ya sa kamfanoni sun samu damar rage sama da kashi 40 na jama’a, daga 30 cikin dari a shekarar da ta gabata.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *