Hukumar kula da ayyukan majalisar tarayya ta amince da ritayar magatakardan majalisar Mohammed Sani-Omolori tare da wasu ma’aikatanta 150.

Shugaban hukumar Ahmed Amshi ya bada sanarwar a cikin wata takarda da ya raba wa manema labarai.

Tun a watan Fabrairu na shekara ta 2020 ya kamata Sani-Omolori ya yi murabus, amma gyaran da majalisar dattawa ta yi wa sharuddan aiki ya sa aka kai shi har tsawon shekaru biyar.

Sai dai Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya Dr Folasade Yemi-Esan, ta bayyana hakan da rashin bin ka’ida tare da take doka.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *