Rundunar ‘yan sandan sun saki dakataccen shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC Ibrahim Magu.

Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja sun ce an saki Magu ne a yammacin Laraban nan.

A makon da ya gabata ne kwamitin da Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa ya fara bincikar Ibrahim Magu bayan shugaban ya dakatar dashi kan zargin almundahana.

Gwamnati ta zargi Magu da gaza bayar da lissafin kuɗaɗen da hukumarsa ta yi iƙirarin ƙwatowa daga hannun waɗanda ta zarga da aikata cin hanci da rashawa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *