Gwamnatin Najeriya ta ce ba yanzu za a maido da sufurin jiragen kasa ba, saboda a cewar ta hakan bai da wani amfani.

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana haka, ya ce akwai hatsari mai yawa musamman idan akayi la’akari da yadda cutar korona ke kara yaduwa cikin al’umma.

Ya ce kowani tarago yana daukar mutane 88, inda koda an rage mutanen zuwa 40 domin bayar da tazara a tsakankanin matafiya, hakan ba karamar asara zai janyo wa Najeriya ba.

Ya kara da cewa Gwamnati na kokarin kiyaye ‘yan Najeriya daga cutar, shiyasa ta ke kara jinkirtawa kadan.

Ministan ya ce akwai sabon jirgi mai gudu da aka siyo mai anfani da diesel.

A cewarsa da zaran an kammala shirye-shiryen fara aiki dashi, Shugaban kasa zai kaddamar dashi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *