Wasu ‘yan bindiga sun sace akalla mutane 30 a yankin Danbushiya da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna.

Wasu mazauna yankin sun tabbatarwa Radiyon Talaka cewa baya ga mutanen da aka sace ‘yan ta’addan sun kashe mutum guda.

Sun ce lamarin ya faru ne tun a lokacin da mazauna kauyukan da ke kewaye suke ribibin komawa gidajensu.

Wani mazaunin yankin ya ce ‘yan bindigar sun yi badda-kama ne ta hanyar sanya kayan sarki, sannan suka datse wata babbar gadar da ke kan hanyar da ta hada garuruwan yankin da Unguwar Millenium City da kuma garin Kaduna.

Ya ce Wadannan mutane suna sanye ne da kayan sojoji, wasu kuma da kayan ‘yan sanda, sa’annan sun tsaya a hanya suna tambayar mutane face-mask, in baka das hi sais u ce ka koma gefe.

Ya ce sun rabu biyu ne, wasu na kan hanya wasu na gefe, in mutum yaje wurin wadanda suke gefe sai su sa ya kwanta.

Ya ce sun yi ta’adi sosai, domin wanda suka kashe ma, lokacin da ya fahinci ba jami’an tsaro ba ne ya yi yunkurin ya gudu, sai suka harbe shi nan take.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *