Shugaban alkalan jihar Kaduna, Muhammad Lawal Bello ya ce a kowace rana ana yi wa akalla mutane 15 fyade a jihar.

Alkalin ya bayyana hakan ne a wajen wani taron da kungiyar lauyoyin Najeriya ta NBA ta shirya a Kaduna.

Ya ce yawancin wadanda ake yi wa fyaden yara ne ‘yan tsakanin watanni uku zuwa shekaru 12.

Ya ce yadda adadin yaran da ake batawa ke kara karuwa abin ban tsoro ne, kuma dole sai an hada hannu an kuma dauki mataki domin a kawo karshen wannan matsala.

Ya kara da cewa, annobar Covid-19 ta tilastawa fannin shari’a gudanar da shari’o’inta ta kafar intanet domin kaucewa jan lokaci wajen kwato wa wadanda aka yi wa fyade ‘yancinsu.

Alkalin ya ce shari’o’i masu tsauri da za su iya kai ga daure mutum gidan yari da hukuncin kisa, za a kaucewa yin su ta Intanet saboda muhimmancin bayyanar shedu a gaban kotu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *