Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bukaci karamain ministan kwadago Festus Keyamo ya ci gaba da shirin daukar aikin da ‘yan majalisar tarayya su ka bukaci a dakatar.

Kwamitin kula da harkokin daukar aiki na majalisar tarayya dai ya dakatar da fara daukar aikin sakamakon hatsaniyar da ta shiga tsakanin su da karamin ministan, oinda a baya su ka kusa ba hammata iska tsakanin su da shi daga bisani su ka kore shi daga majalisar.

Sai dai Keyamo ya zarge su da yunkurin kwace daukar aikin tare da son karbe guraben aikin domin amfanin kan su da makusantan su, ya na mai zargin su da kokarin kalubalantar hukuncin shugaban kasa.

Wata majiya ta ce, Keyamo ya samu ganawa da shugaban kasa, inda ya bayyana ma shi abin da ya faru a majalisar, lamarin da ya sa shugaba Buhari ya fusata da yadda ‘yan majalisar ke son yin katsalandan a lamarin da ya shafi masu zartarwa.

Shugaba Buhari, ya bukaci ministan ya cigaba da shirin, ya kuma tabbatar an yi shi bisa tsarin da ya dace na shari’a.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *