Shugaban rundunar tsaro Janar Gabriel Olonisakin, ya bada tabbacin cewa nan bada jimawa ba matsalar tsaro a yankin Arewa maso yamma, da arewa ta tsakiya zai zama tarihi.

Olonisakin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci runduna ta musamman da aka kafa domin yaki da ayyukan ta’addanci dake da sansani a Faskari, jihar Katsina.

Olonisakin ya ce an kafa rundunar ce domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron lafiya da dukiyoyin al’umma a fadin Najeriya.

Ya ce an kafa rundunar ne bisa kwarewar da za su iya bin ‘yan ta’adda har cikin dazuzzuka a jihohin Katsina, Zamfara, Sokoto, Kaduna da kuma jihar Naija.

Olonisakin ya kuma ba jami’an sojin tabbacin goyon baya da za su ci gaba da samu daga shelkwatar tsaro, domin a cewarsa hakan zai basu kwarin gwiwar ci gaba da yakar ta’addanci.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *