Gwamnatin tarayya ta ce har yanzu bata fara amfani da matsayar rage adadin man da ake fitarwa da aka cimma na kungiyar kasashe masu arzikin man fetur na duniya.

Ministan kula da harkokin man fetur Timipre Sylva ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce har yanzu man da Najeriya ke hakowa yafi adadin da aka amince za ta rika fitarwa.

Ministan ya ce ministocin kasashen sun dau wannan matakin ne domin maido da darajar da man ke da shi a kasashen duniya.

Sylva ya ce akwai shirye-shirye da Najeriya ke kokarin fito dasu domin tabbatar da cewa faduwar darajar man bai haifar da matsala sosai ga tattalin arzikin Najeriya ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *