Hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta ce mutane 595 sun sake kamuwa da cutar korona ranar Litinin, wanda hakan ke nuni da cewa wadanda suka kamu da cutar tun bayan bullar ta a Najeriya suka kai 33,153.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ta shafin ta na twitter a Abuja.

Alkalumman hukumar sun kuma nuna cewa an samu karin mutane 224 da suka warke daga cutar kuma an sallame su daga cibiyoyin killace masu dauke da cutar.

Zuwa yanzu adadin masu korona da suka warke a Najeriya ya kai 13,671, wanda hakan ke nuna cewa yanzu akwai masu cutar korona 19,482 da aka killace a cibiyoyin kwantar da masu cutar a faɗin Najeriya.

An fara gano cutar korona a Najeriya ne a ranar 27 ga watan Fabrairu bayan ya shigo kasar ta filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *