Ministan kula da harkokin sadarwa da fasahar zamani Isa Ali Pantami ya ce aikin jarida na gari na daga cikin ginshikan ci gaban dimokradiyya.

Pantami ya bayyana hakane a lokacin da yake jawabin bude taro wajen horas da kungiyar masu yada labarai na hukumar kula da harkokin fasahar zamani a Abuja.

Ya ce horaswar na daga cikin shirye-shiryen da suke dashi na kara kwarewa kan harkokin fasahar zamani da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu a shekarar 2019.

Ya kara da cewa aikin jarida yanzu bay a ta’allaka ne kawai a buga jaridu ba, akwai sabbin abubuwa da ya kunsa da suka hada da fitar da sakwannin murya, faifan bidiyo da sauran su.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *