Majalisar dattawa ta kafa sabuwar dokar daurin rai-da-rai ga duk wanda aka kama da laifin garkuwa da mutane a Nijeriya.

A dokar wacce Oluremi Tinubu ta gabatar, an yanke shawarar sauya hukuncin ne daga daurin shekaru 10 a gidan Yari zuwa daurin rai-da-rai.

Dokar ta kuma sauya tsarin cewa, wajibi ne duk wadda aka yi wa fyade ta kai kara cikin wani takaitaccen lokaci na watanni biyu ko a karyata ta.

 An kuma sauya tsarin cewa mata kawai ake yi wa fyade, inda a yanzu dokar ta hada da maza, sannan ko an dade da yi wa mutum fyade zai iya shigar da kara kuma a saurare shi.

Rahotanni sun ce yanzu za a tura dokar zuwa majalisar wakilai domin su amince da ita kafin a kai wa shugaban kasa ya sanya mata hannu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *