Kungiyar likitoci ta jihar Legas, na barazanar tafiya yajin aiki a cibiyoyin kula da masu dauke da cutar korona jihar na tsawon kwanaki uku sakamakon rashin biya masu bukatun su.

Shugaban kungiyar Oluwajimi Sodipo wanda ya bayyana wa manema labarai haka, ya ce kungiyarta fara yajin aikin gargadi ne daga ranar 13 zuwa 16 ga watan Yuli.

Sodipo, ya ce bukatun kungiyar sun hada da rashin biyan Likitoci albashin su na tsawon watanni biyu, da bambanta albashin Likitocin da ke aiki da gwamnatin jihar da na gwamnatin tarayya, da rashin biyan su alawus-alawus, da rashin samar da isassun kayan samun kariya daga Korona, da rashin inshorar lafiya da rashin isassun likitoci a asibitocin gwamnatin jihar.

Ya ce kungiyar za ta zauna bayan wa’adin kwanaki ukun da ta bada sun cika domin tattauna matakin da za su dauka a gaba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *