Gwamnatin tarayya ta ce kusan mutane miliyan biyar ne suke son cin moriyar shirin samar da aikin yi ga matasa wanda aka fi sani da N-Power.

Ministar ma’aikatar bayar da agaji da ayyukan gaggawa Sadiya Umar Farouq ta bayyana haka a shafinta na Twitter, ta ce a cikin kwanakin 16 da aka bude shafin da ake karbar takardun neman aikin mutane sama da miliyan 4 suna nema.

Ta kara da cewa ita da ma’aikatanta suna aiki tukuru wajen ganin shirin ya tafi kamar yadda ya kamata.

Ranar 26 ga watan Yunin 2020 aka bude shafin neman aikin na N-Power wanda za a dauki mako shida ana karbar takardun neman aikin  na matasa.

Shirin na N-Power ya gamu da cikas ne tun bayan da  majalisun tarayya suka nemi a dakatar da shirin da gwamnati ta sha alwashin ɗaukar ma’aikata masu ƙaramin ƙarfi 774,000 a dukkanin kananan hukumomin dake fadin kasar nan.

Matakin ya zo ne bayan an samu sabani a tsakaninsu da ƙaramin ministan kwadago Festus Keyamo a lokacin da suka nemi ya yi musu bayani yayin wani zama da suka yi da shi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *