Shugaban rundunar sojin Nijeriya Janar Tukur Buratai, ya ce shi da sauran shugabannin tsaro suna iya bakin kokarin su wajen yaki da ayyukan ta’addanci.

Buratai ya bayyana haka ne, yayin da ya tarbi shugaban ma’aikatar tsaro Janar Gabriel Olanisakin bayan ya kai ziyara sansani na hudu na sojin kasa da ke Faskari a jihar Katsina.

Olanisakin dai ya kai ziyara sansanin ne don ganin yadda aikin atisayen ‘Sahel Sanity’ ke tafiya.

Buratai ya ce, abin jin dadi ne su sanar da shugaban kasa cewa su na matukar godiya a kan karamcin da ya yi masu, ya na mai jaddada cewa ba za su ba shi kunya wajen sauke nauyin da ke wuyan su ba, kuma ba za su ba ‘yan Nijeriya kunya ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *