Kwamitin Majalisar Dokoki ta Jihar Katsina, ya fara gudanar da bincike a kan zargin da ake yi wa gwamnatin jihar na yin almubazzaranci da maƙudan kuɗaɗen da su ka kai naira biliyan 52.

Wasu kungiyoyin farar hula ne su ka buƙaci majalisar ta gudanar da binciken, bayan wani ɗan kasuwa mai Mahdi Shehu ya bijiro da zargin.

Shugaban kwamitin dan majalisa Abduljalal Runka ya shaida wa manema labarai cewa, sun shiga binciken ne da zummar hukunta gwamnatin idan an same ta da laifi ko kuma hukunta Mahdi Shehu idan ƙazafi ya yi mata.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *