Majalisar wakilai ta karbi wani kuduri mai neman a amince da wani tsari da zai ba makarantun allo matsayi tamkar yadda ake ba makarantun boko.

Dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Bodinga, Dange Shuni, da Tureta a jihar Sakkwato Balarabe Shehu Kakale, ya ce ba daliban makarantun allo matsayi zai kara ba su kwarin gwiwa su bayar da tasu gudunmuwa wajen samar da ci gaban kasa.

A cewar sa mafi yawa daga cikin wadannan daliban suna da basira da hukumomi za su yi amfani da su wajen gina kasa.

Dr. Umar Altine Dadin Mahe, sakataren zartaswa na hukumar larabci da addinin musulunci, ya ce wannan tsari idan aka amince da shi a matakin kasa zai taimakawa jihohi kamar jihar Sokoto wadda dama ta kudurci sake fasalin tsarin almajirci ta yadda dalibai za su daina bara.

Farfesa Tukur Muhammad Baba, na sashen nazarin halayyar Dan Adam a jami’ar gwamnatin tarayya da ke Birnin Kebbi ya ce tsarin yana da kyau amma sai an cire batun siyasa ko addini sannan a yi masa kwakkwaran tsari ta yadda kwalliya za ta biya kudin sabulu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *