Wani lauya mai rajin kare hakkin bil adama, Kabir Akingbolu, ya ce ministan shari’a, Abubakar Malami, na iya fuskanatar hukuncin daurin shekaru biyar sakamakon sai da gangunan man fetur ba bisa ka’ida ba.

Lauyan ya ce Malami ya ba da umarnin sayar da kadarorin ne, bayan jami’an tsaro sun kwatosu daga hannun barayin man fetur a yankin Naija Delta.

Wannan na zuwa ne bayan wasu rahotanni sun bayyana wata takarda da ke nuna cewa Malami ya ba da umarnin sai da wasu manyan gangunan danyen man fetur ga wani kamfani.

Majiyar ta ce Malami ya bada umurnin sai da man ne ga wani kamfani mai suna ‘Omoh-Jay’ duk da tuhumar da ake yiwa kamfanin da zargin barnatar da metrik ton 12,000 na danyen man fetur a shekarar 2009.

Sai dai ministan shari’ar, Malami ya ce ba laifi bane don ya ba da umarnin a yi gwanjon danyen man.

Malami ya ce sashe na 36 da biyar a cikin baka na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 ya ba kamfanin damar shiga ciniki ko dillancin man fetur a Najeriya saboda ya na da rijista da gwamnati kuma har yanzu kotu ba ta sameshi da laifi ba a tuhumar da ake yi ma sa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *