Wani kamfanin samar da takin zamani domin manoma na kasar Amurka zai bude reshen kamfanin na Afrika a jihar Kebbi.

Jami’ar kula da harkokin kasuwanci na kamfanin a Najeriya Bill Stevens, ta bayyana haka a lokacin da take ganawa da dukkanin kungiyoyin manoma dake jihar.

A cewarta idan aka kammala samar da kamfanin na Najeriya zai dauki ma’aikata akalla dubu daya.

Ta ce a baya kamfanin ya so samar da cibiyar ne a kasar Afrika ta kudu, inda daga bisani ya canza shawarar dawowa Najeriya.

Stevens, ta ce gwamnatin tarayya da hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya sun san da shirye-shiryen da kamfanin yake dashi tun a shekarar 2014.

Ta kara da cewa an gudanar da gwajin amfani da takin da kamfanin ke samarwa a jihohin Kwara, Zamfara, Sokoto, Kaduna da Kebbi, kuma alamu sun nuna cewa za a samu amfani mai yawan gaske.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *