Tubabbun ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram dari 6 da 2 sun yi rantsuwar ficewa daga kungiyar tare da rungumar dabi’u na gari ta yadda za su amfani Najeriya.

Tubabbun ‘yan ta’addan sun dau rantsuwar ne a sansanin Malam Sidi dake karamar hukumar Kwami a jihar Borno bayan sun kammala shirin da aka kirkiro domin saisaita tunanin su.

Mutanen sun dau wannan matakin ne a gaban kwamitin shari’a na mutane 11, karkashin mai shari’a Nehizena Afolabi na babbar kotun Gombe.

A lokacin da yake magana shugaban runduna ta musamman dake yaki da ayyukan ta’addanci da ake yiwa lakabi da  Operation Safe Corridor, Majo Janar Bamide Shafa, ya ce bayyana datubabbun ‘yan ta’addan suka yi a gaban alkalan na daya daga cikin matakan da suka kamata a dauka kafin barinsu su shiga cikin al’umma.  

Shafa ya ce tun bayan kaddamar da shirin yin afuwar a shekarar 2016 an dauki mutane dari 8 da 93 a sansanin da a cikin su aka maida wasu dari 2 da 80 kasashen da suka fito.

Ita ma a nata jawabin kwamishinan kula da harkokin mata da ci gaban al’umma ta jihar Borno, Zuwaira Gambo, ta ce akwai shiri na musamman da gwamnatin jihar ta yi domin ci gaba daga inda aka tsaya na horas da tubabbun ‘yan ta’addan.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *