Hukumar kiyaye aukuwar haddura ta kasa reshen babban birnin tarayya Abuja ta bukaci kungiyoyin sufuri su rika bin dokokin kariya tare da dakile yaduwar cutar korona.

Kwamandan hukumar a Abuja Gora Wobin, ya bukaci hakan a lokacin da yake ganawa da shugabannin kungiyoyin a Abuja.

Wobin ya ce akwai bukatar ana a rika bin dokokin kariya dari bisa dari kamar yadda hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta bukata a daidai lokacin da aka sassauta dokar hana zirga-zirga a tsakanin jihohi.

Sannan ya bukaci kungiyoyin su rika bin dokokin hukumarsa domin dakile yaduwar cutar tare da tabbatar da cewa an yake ta baki daya.

A cewarsa sassauta dokar da gwamnatin tarayya ta yi dama ce na a hada hannu a dukkanin bangarori wajen dakile yaduwar cutar baki daya.

Wobin ya ce daukar matakin yin nesa-nesa da juna, da rage yawan fasinjojin da ake dauka da kashi 50 cikin dari, da kuma amfani da takunkumin rufe hanci da baki zai taimaka matuka wajen dakile yaduwar cutar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *