Gwamnatin tarayya ta fara raba kayayyakin tallafi ga ‘yan gudun hijira da ayyukan ta’addanci ya raba da muhallansu a sansanin su dake Zangon Jema a karamar hukumar Goronyon jihar Sokoto.

A lokacin da yake kaddamar da rabon kayayyakin kwamishinan hukumar Bashir Garba, ya ce an samar da kayayyakin tallafin ne domin amfanin ‘yan gudun hijira dari 3 da 50 dake sansanin.

Ya ce wannan na daga cikin kudurin da gwamnatin tarayya ke da shi na sassauta musu halin matsi da suka tsinci kawunansu a ciki bayan ‘yan ta’adda sun raba su da gidajensu.

Garba wanda ya samu wakilcin mataimakin daraktan hukumar mai kula da yankin Arewa maso yammacin kasar nan Musa Kangiwa, ya godewa gwamnatin jihar bisa irin tarbar da suka samu.

Sannan ya bukaci ‘yan gudun hijiran da su dauki abubuwan da suka faru dasu a matsayin jarabawar Ubangiji, tare da amfani da kayayyakin da suka samu ta hanya mai kyau.

Kayayyakin da aka raba sun hada da shinkafa, wake, masara, dauro, man gyada, gishiri, tumatiri da sauran su.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *